Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta HRW, ta ce ci gaba da kasuwanci da yankunan da Isra’ila ta mamaye tamakar cin zarafin dan adam ne, kuma dole a kawo karshensa.
A game da hakan ne kungiyar ta bukaci kwamitin kungiyar tarayyar turai, da ya haramta duk wani kasuwanci da yankunan da dake karkashin mamayar Isra’ila musamman na Faladinawa, saboda hakan a cewarta tamakar laifukan yaki ne.
Wasu alkalumma da bankin duniya ya fitar a shekarar 2012, sun nuna cewa kayayacin kasuwanci da kungiyar EU, ke shigar dasu zuwa yankunan falasdinawa da Isra’ila ta mamaye sun kai kusan na Dala Miliyan 300.
342/